Sojoji uku da wasu mutum bakwai sun kwanta dama a musayar wuta da ’yan bindiga a kauyen Kabasa da ke Karamar Hukumar Gusau ta Jihar Zamfara.
Mazauna garin sun shaida wa Aminiya cewa ’yan bindigar sun je garin ne a kan babura suna yi wa mutane ruwan wuta a ranar Talata.
- Yaro mafi kiba a duniya ya rage nauyi da kilo 107
- Zazzafar muhawara ta barke a Majalisa kan wani sabon kudiri
- Mahara sun bindige mutum 55 a Nijar
Wani ganau ya ce, “Mun shiga dimuwa inda aka raunata wasu daga cikin mazauna da ke kokarin tserewa; An kuma tabbatar da mutuwar mutum bakwai a harin.”
Gwamna Bello Muhammad Matawalle ya bayyana kaduwa game da harin kan mutanen da babu ruwansu a kauyen Kabasa da ke gundumar Magami.
Matwalle, ta bakin ta bakin kwamishinan yada labarai Alhaji Ibrahim Dosara ya ce ya yi bakin cikin yadda harin ya haifar da asarar rayuka a kauyen kuma ya yi Allah wadai da hakan.
Gwamnan ya kuma mika ta’aziya ga dangin wadanda abin ya shafa tare da yin addu’ar Allah Ya rahamshe su.
“Tuni gwamnati ta umarci hukumomin tsaro a jihar da su gudanar da cikakken bincike kan lamarin sannan su kawo mata rahoto don daukar mataki.
“Kwamitin tantance barnar da gwamnatin jihar ta kafa kuma, an umarce shi da ya ziyarci al’ummar domin tantance irin barnar da aka yi musu.”
Yunkurinmu na jin ta bakin sojojin ya ci tura; Kakakin rundunar ‘Operation Hadarin Daji’ Kaftin Ibrahim Yahaya bai amsa kiraye-kiraye da wakilinmu ya yi ba a lokacin hada wannan rahoton.