✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun kashe Shugabannin Fulani

’Yan sanda sun tabbatar da harbe shugabannin kungiyar Miyetti Allah a cikin kasuwa a Nasarawa.

’Yan bindiga sun harbe Shugaban Kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti Allah, reshen Jihar Nasarawa, Alhaji Mohammed Hussain, tare da Shugaban Kungiyar na Karamar Hukumar Toto, Mohammed Umar.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Nasarawa, Ramham Nansel, ya tabbatar cewa maharan sun bindige Shugabannin Kungiyar ne a kasuwar, ranar Juma’a da dare.

“Da misalin karfe 7 na dare ranar 2 ga Afrilu, 2021 cewa ’yan bindiga da ake zargi Fulani ne sun kai hari sun kashe Shugaban Kungiyar Miyetti Allah na Jihar Nasarawa, Mohammed Hussaini, da kuma Mohammed Umar, Shugaban Kungiyar na Karamar Hukumar Toto a Kasuwar Garaku.

“Bayan samun labarin, Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Nasarawa, Bola Longe ya tura jami’an Rundunar Operation Puff Adder II suka je wurin suka dauke gawarwakin suka kai asibiti,” inji shi.