✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun kashe shugaban yakin nema zaben APC a Ribas

An tsinci gawarsa ce kwance cikin jini da ramukan harbin bindiga

Wasu ’yan bindiga da suka sace shugaban kwamitin yakin neman zaben jam’iyyar APC na karamar hukumar Ahoada ta Yamma a Jihar Ribas, Chisom Lennard, sun harbe shi har lahira.

’Yan bindigar da suka sace Lennard sun dira ne a rumfar zaben Ibagwa 2, da ke karamar hukumar sanye da kayan ’yan sanda ana tsaka da zaben gwamna da majalisar jiha.

Kakakin jam’iyyar a jihar Darlington Nwauju ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce Chisom ya yi yunkurin hana ’yan bindigar sace kayayyakin zabe ne, daga nan ne kuma suka dauke shi suka tafi da shi.

“Ba wanda ya san inda suka kai shi, sai jiya da yamma ne aka tsinci gawarsa”, in ji shi.

An dai tsinto gawar tasa ce kwance cikin jini, da ramukan harbin bindiga a kan hanyar Ibueahi-Ubeta da ke karamar hukumar ta Ahoada.