✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun kashe sama da mutum 50 a kauyakun Kaduna

Majaran sun kuma sace mutane da dama yayin harin

Wasu ’yan bindiga sun kai hari a kauyaku tara na Karamar Hukumar Giwa ta jihar Kaduna inda suka kashe sama da mutum 50, sannan suka sace wasu da dama.

Wani mazunin yakin da Aminiya, ta tattauna da shi kuma ya nemi a sakaya sunansa ya ce lamarin ya auku ne a daren Alhamis zuwa wayewar garin Juma’a.

Ganau din ya ce tun da misalin karfe 7:00 na yamma ne aka fara ganin bakin a kan babura dauke da bindigu, kuma an yi kokarin samar da jami’an tsaro.

Kauyakun da ’yan bindiga suka kutsa sune, auguwar Kaya Fatika, Barebari Dillale, Zangon Tama, Anguwar Bakko, Gidan Alhajin Kida da kauyan Kadanya da Doromi, duk a cikin karamar hukumar ta Giwa.

Kazalika, sun kuma kona gidaje kusan 40 da motoci 30 da kuma wata majami’a a kauyen zangon Tama.

’Yan bindigar sun kuma raunata mutane da dama da harbin bindiga, inda wasu ke kwance a Asbiti Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello (ABUTH) da ke Shika, suna samun kulawa.

Aminiya ta ziyarci asibitin inda wakikinmu ya gane wa idonsa mutum uku masu raunin harbin bindiga.

Mutanen sun hada da Abubakar Usman daga anguwar Bakko da Alhaji Sa’idu da kuma Malam Hari da ya rasu.

Ko da wakilin namu ya ziyarci Karamar Hukumar ta Giwa, ya tarar da Shugabanta da mukarrabansa sun tafi babban taron jam’iyar APC a Abuja.

Sai dai kakakin Rundunar ’Yan Sandar Jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige, ya tabbatar da faruwar lamarin sai dai ya ce yana jiran karin bayanin daga Baturen ’Yan Sanda (DPO) na Giwa.

%d bloggers like this: