✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun kashe mutum uku a Katsina

’Yan bindiga sun kashe mutum uku a wani sabon hari a Karamar Hukumar Dandume ta jihar Katsina. Da safiyar Litinin din nan ne maharan dauke…

’Yan bindiga sun kashe mutum uku a wani sabon hari a Karamar Hukumar Dandume ta jihar Katsina.

Da safiyar Litinin din nan ne maharan dauke da muggan makamai suka auka wa kauyen Maikwama, inda suka saci dabbobi da da kayan abinci bayan sun kashe mutum uku.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Katsina ba ta kai ga cewa komai game da harin ba tukuna.

Harin na Dandume na zuwa ne a washegarin ranar da ’yan bindiga suka kai hari a kauyen Kurmin Chakara inda suka yi garkuwa da wani mai suna Alhaji Kabiru.