✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kashe mutum huɗu a Kogi

An buƙaci hukumomin tsaro da su jibge jami’ansu a wuraren da ke da rauni domin razanar da masu mugun nufi.

Akalla mutum huɗu aka tabbatar sun riga mu gidan gaskiya a sakamakon wani harin ’yan bindiga a yankin Agojeju-Odu na gundumar Bagaji-Odoh da ke Karamar Hukumar Omala a Jihar Kogi.

Dan Majalisar Dokokin jihar mai wakiltar Karamar Hukumar Omala, Honarabul Umar Yahaya ne ya bayyana hakan bayan miƙa wa Gwamna Usman Ahmed Ododo rahoton faruwar lamarin a ranar Laraba a Lokoja.

Honarabul Yahaya wanda ya yi Allah-wadai da faruwar lamarin, ya ce ’yan bindigar da suka aikata wannan ta’asa sun haura mutum 100 a yayin harin.

Ya bayyana cewa harin ya auku ne da misalin ƙarfe 3:30 na Yammacin ranar Talata, 30 ga watan Janairu, inda ’yan bindigar suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi.

Dan majalisar ya ce ’yan bindigar sun mamaye kauyen ne ta Gabas inda suka shigo ta makwabtakan garuruwan da ke iyaka da jihohin Nasarawa da Benuwe.

Yahaya ya bayyana cewa, a yayin harin, akwai wata mata da ke jinya a wani asibitin kuɗi da aka yi wa yankan rago.

“Akwai kuma wasu mutum biyu, Mista Attai John Idagboyi da wani Mista Daniel Shuaibu da aka yi wa kisan wulakanci.

“An kuma tsinto gawar wani mutum da aka sassar a jeji, inda aka samu mutum huɗu jimilla da aka kashe, wato maza uku da mace daya.”

Dan majalisar ya roƙi gwamnatin jihar da ta tabbatar Kwamishinan ’Yan sanda, CP Benthrand Onuoha da sauran jagororin hukumomin tsaro sun jibge jami’ansu a wuraren da lamarin ya shafa domin kwantar da tarzoma.

A cewarsa, kasancewar jami’an tsaro a irin wannan wurare yana razanar da duk wasu masu mugun nufi da ke yunkurin dugunzuma hankulan jama’a.

Kazalika, ya buƙaci Gwamna Ododo da ya bai wa Hukumar Bayar da Agaji ta jihar umarnin tallafa wa wadanda lamarin ya shafa da kayayyaki domin rage raɗaɗin halin da suka shiga.