Mahara sun kashe mutane akalla 20 a harin da suka kai daren Laraba a Karamar Hukumar Zankon Kataf ta Jihar Kaduna.
Mutane da dama sun bace bayan harin na kauyukan Apyiashyim, Atak’mawai, Kibori, da kuma Kurmin Masara a Masarautar Atyap.
Da na fara jin harbe-harbe sai na kwashi iyalaina muka gudu domin mu tsira.
“An kashe mutum 13 yawancinsu mata da kananan yara”, inji wani mazaunin Atak’mawai wanda ya ce maharan sun shiga kauyensu da misalin 1.00 na dare.
Wani mazaunin Apiashyim, Jonathan Ishaya ya ce ‘yan bindigar sun kashe mutum shida suka kuma kona kusan rabin gidajen kauyen.
Ya ce maharan sun far wa kauyen ne da misalin 11.00 na daren suka yi ta harbi kan mai uwa da wabi.
Wakilinmu ya gano cewa ‘yan bindigar sun kashe musun 13 a Kurmin Masara inda suka kona gidaje da dama.
A kauyen Kibori kuma mutum shida ne suka mutu aka kuma kona gidaje 10.
Maharan sun kuma kashe mutum uku a Mawai Zango inda suka cinna wa gidaje bakwai wuta.
Zuwa lokacin hada wannan rahoton akilinmu bai kai ga samun Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kaduna domin karin bayani game da lamarin.
Harin na zuwa ne bayan a ranar Talata an kai wa wasu Fulani makiyaya hari a lokacin da suke kiwo a kauyen Gora Gan a Karamar Hukumar.
Makiyayan sun tsallake rijiya da bayan da raunin bindiga, lamarin da ya sa aka kwantar da su a asibiti.
Ricikin yankin Kudancin Kaduna ya kara kazancewa a baya-bayan nan, inda ake yawan samu hare-hare da kuma daukar fansa tsakanin kabilu.