✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun kashe mutum daya, sun sace 15 a Neja

Sun rika bi gida-gida suna dibar dukiya musamman kayayyakin abinci.

Rahotanni sun bulla cewa ’yan bindiga sun kashe wani mutum daya sannan sun yi awon gaba da wasu mutane kimanin 15 a kauyen Batagari da ke gundumar Maikujeru a Karamar Hukumar Rafi ta Jihar Neja.

Aminiya ta ruwaito cewa, ’yan bindigar sun kai harin ne da yammacin ranar Lahadi, inda galibi mutanen da suka yi awon gaba da su mata ne.

Wata majiya mai tushe da ta zanta da wakilinmu, ta bayar da shaidar cewa, ’yan bindigar sun kai harin ne haye a kan babura inda suka rika harbe-harbe a iska domin razana mutanen kauyen.

A cewar majiyar, bayan sun firgita al’umma, sai suka fara bi gida-gida suna dibar dukiya musamman kayayyakin abinci.

Haka kuma, wata majiyar ta ce har yanzu ’yan bindigar ba su soma tuntubar ’yan uwan wadanda suka yi garkuwar da su ba.

Sai dai hakar da wakilinmu ya yi ba ta cimma ruwa ba a kokarinsa na jin ta bakin mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar, DSP Wasiu Abiodun.