’Yan bindiga sun kashe mutum tara tare da raunata wasu biyar, gami da sace dabobbi 250, a wasu hare-hare da suka kai a kananan hukumomin Igabi da Zariya a Jihar Kaduna.
Tun da farko an rawaito cewa ’yan bindigar sun kai hari yankin Kudu da Gari da ke Karamar Hukumar Igabi, inda suka kashe mutum bakwai.
- Za a fara yanke wa masu garkuwa da mutane hukuncin kisa a Filato – Lalong
- An kai wa gidan dan sanda mai yaki da ’yan ta’adda hari a Zariya
Sun kuma raunata mutum hudu, wadanda tuni an garzaya da su asibiti domin ba su kulawa.
A wani harin kuma, ’yan bindiga sun farmarki Ruggar Goshe, Kangimin Sarki, da Rigachikun, inda suka kashe mutum daya sannan suka yi awon gaba da dabobbi 250.
Kazalika, sun kai hari rugar Filin Idin Barebare da ke Zariya, inda suka kashe mutum daya sannan suka harbi wani a kirji, wanda tuni aka garzaya da shi zuwa asibiti.
Har wa yau, an rawaito ‘yan bindigar sun sace dabobbi masu dinbim yawa wanda ake kyautaya zaton sun kai 250.
Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida Cmna Jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya tabbatar da faruwar harin cikin wata sanarwa da ya fitar.
Amma ya ce jami’an tsaro sun yi nasarar kashe ’yan bindiga biyu da suka farmaki kauyukan Tumbau da Kerawa a Karamar Hukumar Igabi.
Ya ce ’yan bindigar na kokarin tserewa dajin Malul da ke Jihar, yayin da jami’an tsaro suka kai musu samame suka bude musu wuta, kazalika an kwace bindigogi kirar AK47 guda biyu daga wajensu.
Kwamishinan ya ce gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi addu’a ga wadanda suka rasa rayukansu sannan ya jajanta wa iyalan sauran wadanda abun ya shafa.
Aminiya ta rawaito yadda mahara suka kai hari a ranar Lahadi, inda suka kashe akalla mutum bakwai tare sa sace wasu 40 a wasu hare-hare a Jihar Kaduna.