’Yan bindiga sun kashe mutum takwas yayin wani hari na daren ranar Talata da suka kai kauyen Wumat da ke Karamar Hukumar Bokkos a Jihar Filato.
Wani mazaunin kauyen mai suna Adamu Isa ya shaida wa Aminiya cewa, ‘yan bindigar sun kai farmakin ne da misalin karfe 10 na dare, inda suka fara harbe-harbe don tarwatsa masu kai komo, wanda a sanadiyar haka ajali ya katse hanzarin mutanen takwas.
- Dan bindiga ya harbe mutum 10 a kantin sayar da kaya a Amurka
- Turji ya tsare ’yan aike bayan sun kai masa harajin N10m
Isa ya ce “Yawan wadanda suka mutu zai iya haura takwas saboda an garzaya da wadanda suka jikkata zuwa asibiti.
Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Alabo Alfred, ya ce ba shi da masaniya kan aukuwar harin sai dai ya ce zai binciki lamarin.
Harin na baya-bayan nan dai na zuwa ne kwanaki bakwai bayan da wasu ‘yan bindiga suka kashe mutane 11 tare da raunata wasu a unguwar Maikatako da ke Karamar Hukumar Bokkos a jihar ta Filato.
Jihar Filato na ci gaba da fama da fadace-fadacen kabilanci da kuma ayyukan ’yan bindiga da bata-gari.