Aƙalla mutum shida ne aka ruwaito cewar sun rasu bayan da ’yan bindiga suka kai hari ƙauyukan Bauda da Chibiya da ke gundumar Maro a ƙaramar hukumar Kajuru a Jihar Kaduna.
’Yan bindigar sun kai hari ƙauyukan biyu ne a ranar Litinin da yamma, inda suka kashe mutum shida.
- An kama ƙasurgumin ɗan ta’adda a Yobe
- DAGA LARABA: Yadda Kanawa Suka Je Kallon Hawan Daushe A Zazzau
Daga baya maharan sun yi awon gaba da mutanen da ba a tantance adadinsu ba.
Kazalika mutane da dama sun samu raunuka a yayin harin.
Har yanzu rundunar ’yan sandan jihar, ba ta ce uffan ba kan faruwar lamarin ba, amma shugaban ƙaramar hukumar Kajuru, Ibrahim Gajere, ya ce ’yan bindigar sun mamaye yankunan ne a kan babura, inda nan take suka harbe mutum biyu a ƙauyen Bauda.
Ya ce daga baya ’yan bindigar sun sake kashe wasu mutum huɗu a ƙauyen Chibiya, daga ciki har da wani baƙo da ya kai ziyara ƙauyen.
Shugaban ƙaramar hukumar, cikin wata sanarwa da ya fitar, ya bayyana cewa maharan sun kashe mutum huɗu a gonakinsu yayin da suka hallaka wasu mutum biyu a gidajensu.
Shugaban ya kuma bayyana cewa ’yan bindigar sun ƙone gidaje kusan bakwai tare da babura takwas a yankunan.
Ya ce an sanar da jami’an tsaro faruwar lamarin, kuma tuni suka tsaurara tsaro a ciki da wajen yankunan.