✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kashe mutum 6, sun raunata sojoji a Binuwai

Maharan sun dauki tsawon minti 30 suna artabu da sojoji.

Mahara sun kashe wasu kauyawa shida tare da raunata sojoji uku a wani sabon hari a yankin Ikobi a Karamar Hukumar Apa a Jihar Binuwai.

Majiya mai tushe ta shaida wa wakilinmu a Makurdi cewa an kashe soja daya sannan wasu abokan aikinsa biyu sun samu munanan raunuka bayan da suka yi arangama da ’yan bindigar da suka mamaye yankunan karkara a karshen mako.

Amma rundunar sojin ta tabbatar da cewa sojoji uku sun samu raunuka a arangamar da suka yi da ‘yan bindiga.

Daya daga cikin mazauna yankin ya ce sojojin rundunar ‘Operation Whirl Stroke’ (OPWS) da ke Agagbe sun amsa kiran gaggawa inda suka yi arangama a Tse-Abwa da ke Karamar Hukumar Gwer ta Yamma.

Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Apa, Abu Umoru, ya tabbatar wa da wakilinmu faruwar harin.

Umoru ya ce, “Hakika ya faru, mutanen da ake zargin makiyaya ne sun mamaye yankin Ikobi kuma ya zuwa yanzu an yi asarar rayuka shida cikin kwanaki hudu da suka gabata. Za a iya samun karin wadanda suka mutu.

“Mutane sun tsere daga gidajensu, saboda gudun harin ’yan bindigar.”

Kakakin ’yan sandan jihar, SP Catherine Anene, ta ce ba ta da labarin faruwar harin.

Kakakin rundunar ‘Operation Whirl Stroke (OPWS)’, Laftanar Katty Audu, ta tabbatar da harin wanda ya yi sanadin jikkata sojoji uku.

Ya ce, “Dakarun sun samu labarin harin da aka kai wa al’ummar Ikobi a ranar 4 ga Fabrairu, 2023, da misalin karfe 5 na yamma kuma sun kai dauki. Makiyayan dauke da makamai sun tsere zuwa Jihar Nasarawa bayan sun hangi dakarun.

“’Yan bindigar sun bude wa sojoji wuta inda su ma suka mayar da martani inda aka dauki tsawon mintuna 30 ana barin wuta.

“Uku daga cikin sojojinmu sun samu raunuka. Sojojin da suka jikkata a halin yanzu ana ba su kulawa.”