✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘Yan bindiga sun kashe mutum 6 a Kogi

‘Yan bindiga sun kashe mutum shida a Jihar Kogi, ciki har da Sufeton ‘yan sanda biyu da ‘yan kasar waje biyu yayin harin da suka…

‘Yan bindiga sun kashe mutum shida a Jihar Kogi, ciki har da Sufeton ‘yan sanda biyu da ‘yan kasar waje biyu yayin harin da suka kai wa tawagarsu a ranar Juma’a.

Haka nan, direbobin ‘yan ketaren biyu na daga cikin wadanda suka rasa ransu a harin.

Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, SP William Ovye-Aya, shi ne ya bayyana haka cikin sanarwar da ya fitar ranar Asabar a Lokoja, babban birnin jihar.

Ovye-Aya ya ce wadanda lamarin ya shafa sun cimma ajali ne yayin musayar wuta da ‘yan bindigar a hanyar Lokoja-Ajaokuta da misalin karfe 8 na dare na ranar Juma’a.

A cewarsa, ‘yan bindigar sun yi wa tawagar kwanton-bauna ne sa’ilin da ‘yan sandan ke yi wa ‘yan ketaren rakiya zuwa wani kamfaninsu da ke Ajaokuta.

Ya ce sai da aka hada karfi tsakanin ‘yan sandan yankin da sosjoji kafin aka samu nasarar korar ‘yan ta’addan.

Ya kara da cewa, tuni Kwamishinan ‘Yan sandan Jihar, CP Edward Egbuka ya ziyarci wurin da harin ya auku don gane wa idanunsa abin da ya faru.

Kazalika, ya ce Kwamishinan ya ba da umarnin a tura karin jami’ai zuwa yankin don kwantar da tarzoma.

(NAN)

%d bloggers like this: