Akalla mutane biyar ne ‘yan bindiga suka hallaka da sanyin safiyar ranar Lahadi a wurere daban-daban a kananan hukumomi biyu dake jihar Binuwai.
Wakilinmu ya rawaito cewa ‘yan bindigar sun yi kutse ne cikin gidan tsohon dan majalisar jihar mai wakiltar Karamar Hukumar Katsina-Ala ta gabas dake kauyen Nagu, Inna Jato inda suka kashe uku daga cikin mutum biyar din.
- An kashe basarake mako daya bayan garkuwa da shi a Neja
- Isra’ila: An kama masu zanga-zangar adawa da Netanyahu
- Ba ni da shirin ficewa daga PDP – Gwamnan Abiya
Ragowar biyun ana zargin kisan nasu na da alaka da ‘yan kungiyar asiri a yankin Naka cikin karamar hukumar Gwer ta Arewa.
Wadanda lamarin ya faru akan idonsu, sun bayyana cewa ‘yan ta’addar sun kai wasu farmakin a wasu wurare biyu, inda suka lalata dukiyoyi da kona gidaje da dama, ciki har da gidan tsohon dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Katsina-Ala.
Jami’in Watsa Labaran Shugaban Karamar Hukumar Katsina-Ala, Tertsea Benga, ya tabbatar da kisan mutane ukun da ‘yan bindigar suka kashe a gidan tsohon dan majalisar jihar.