Wasu ’yan bindiga sun kashe akalla mutum 41 da ake kyautata zaton ’yan kungiyar sa-kai ne a Karamar Hukumar Bakori ta Jihar Katsina.
Wadanda lamarin ya rutsa da su kamar yadda Aminiya ta samu rahoto, sun fita ne da nufin kwato dabbobinsu da ’yan bindigar suka sace.
- Zanga-zanga ta barke a Kudancin Najeriya saboda karancin sabuwar Naira
- Za mu dage mulkin Najeriya ya koma hannun mutanen Kudu a Zaben 2023 —El-Rufai
Sai dai labari ya shan bamban yayin da ’yan bindigar suka yi wa jama’ar kwanton bauna wanda a dalilin haka mutum 41 daga cikinsu suka bakunci lahira sannan da dama suka jikkata.
Rundunar ’yan sandan Jihar Katsina ta bakin mai magana da yawunta, SP Gambo Isa ta ce, a ranar Laraba ce ’yan bindigar suka kai hari gidan wani Alhaji Muntari a Unguwar Audu Gare da ke kauyen Kandarawa a Karamar Hukumar ta Bakori.
SP Gambo ya ce ’yan bindigar sun yi awon gaba da dabbobi bayan harbe-harbe kan mai uwa da wabi domin razana mazauna kauyen.
Wakilinmu ya ruwaito cewa, hakan ya janyo kungiyar ’yan sa-kan daga kauyuka 11 suka fita domin tunkurar ’yan bindigar a dajin ganin yadda tura ta kai bango.
Bayanai sun ce ’yan sa-kan sun yi kicibus ne da ’yan bindigar dajin ’Yargoje kuma babu wata-wata mutum 41 suka ce ga garinku nan.
Ya zuwa hada wannan rahoto, tuni an kwantar da wadanda suka jikkata a Babban Asibitin Kankara inda suke samun kulawa.