’Yan bindiga sun kashe mutum 30 da talatainin daren Talata a kauyen Tanknale da ke Karama Hukumar Mangu ta jihar Filato.
Kakakin ‘yan sandan jihar, DSP Alfred Alabo, ya ce bayan samu rahoton cewa maharan suna harbi babu kakkautawa a kauyen ne, ‘yan sanda suka kai dauki aka fatattaki maharan wadanda har yanzu kai ga gano daga inda suka fito ba.
- ’Yan Arewa ke jefa yankin cikin jahilci —Ministan Ilimi
- Ainihin dalilin ganawar Tinubu da Kwankwaso da Sanusi II a Faransa
Sanarwar da Alabo ya fitar ta ce rundunar ‘yan sandan jihar da sauran hukumomin tsaro na yin duk mai yiwuwa domin ganowa da kuma kamo masu hannu a harin don su fuskanci hukunci.
A yayin da ya ziyarci kauyen, Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda Mai Kula da Binciken Manyan Laifuka na jihar, Bawa Sale, ya ce maharan sun tsere sun bar motarsu daya da babura guda hudu.
Ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar ya bukaci jama’r yankin su kwantar da hankalinsu, jami’an tsaro na aiki domin cafke ‘yan bindigar.
Ya kuma yi kira gare su da su rika ba wa jami’an tsaro bayanai a kan lokaci domin daukar mataki da wuri.