✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun kashe mutum 3 suna tsaka da bude-baki a masallacin Taraba

Maharan sun kuma yi awon gaba da wasu mazauna garin da dama

Wasu ’yan bindiga sun kashe mutum uku a lokacin suke bude-baki a cikin wani masallaci a garin Baba Juli da ke Karamar Hukumar Bali a Jihar Taraba.

Lamarin ya faru ne ranar Talata da misalin karfe 6:25, a lokacin da suke bude-baki.

’Yan ta’addan kimanin su 50 an ce sun auka wa kauyen sannan suka bude musu wuta.

Wani mazaunin kauyen wanda bai amince a ambaci sunansa ba, ya shaida wa Aminiya cewa ’yan ta’addan, bayan sun kashe mutum uku a cikin masallacin, sun kuma yi awon gaba da wasu mutane masu yawa daga kauyen, kuma har yanzu ba a ji duriyarsu ba.

Ya Kuma ce ’yan taaddan sun taba kai wa kauyen hari a cikin watan Maris, amma ba su yi nasara ba domin a wancan lokacin mazauna kauyen sun fito sun tunkare su.

Mutumin ya kuma ce harin na ranar Talata ya zo masu da ba-zata domin suna cikin bude baki lokacin da aka kawo harin.

Kakakin Rundunar ’Yan Sanda na Jihar, DSP Usman Abdullahi, ya ce bai sami labarin wannan hari daga ofishin shiyyar Bali ba, amma zai bincika.