Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce sabon harin ‘yan bindiga ya yi sanadiyar mutuwar mutum uku da raunata mutum daya a Karamar Hukumar Zangon-Kataf ta jihar.
Mista Samuel Aruwan, Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida ne ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin a Kaduna.
- A dauki mataki kan kisan matafiya a Jos — FOMWAN
- Ba ni da sha’awar zama Shugaban Kasa — Sarki Sanusi
“Gwamnatin Jihar Kaduna ta samu cikakken bayani kan harin da aka kai a Goran Gida, gundumar Gora ta Karamar Hukumar Zangon-Kataf, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mazauna garin guda uku da jikkatar wani mutum daya.”
Aruwan ya ce maharan sun shiga kauyen ne a daren ranar Lahadi inda suka kashe mutum uku, yana mai cewa wanda aka jikkatar yana karbar magani.
“Maharan sun kone mota daya a yayin da a halin yanzu hukumomin tsaro ke ci gaba da sintiri a yankin,”in ji Aruwan.
A cewarsa, Mataimakiyar Gwamnan Jihar, Dokta Hadiza Balarabe, ta karbi rahoton cikin bacin rai tare da yin Allah wadai da harin da aka kai kan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.
Hadiza ta jajanta wa iyalan mamatan ta kuma yi musu addu’ar Allah Ya jikansu tare da yi wa wanda ya ji rauni fatan samun sauki cikin gaggawa.