Wasu ’yan bindiga sun kai hari kan wasu kauyuka da ke Karamar Hukumar Bukkuyum ta Jihar Zamfara, inda suka kashe akalla mutum 26, sannan suka yi awon gaba dabbobi da yawa.
Wani mazaunin garin Bukkuyum ya bayyana cewa ’yan bindigar da adadinsu ya kai 100 sun hallaka akalla mutum sama da 20.
- Sojoji: Har yanzu akwai aiki babba a gabanku — Buhari
- Karin mutum miliyan bakwai sun fada talauci a Najeriya —Bankin Duniya
Mutumin da ke zaune a kauyen Babban Maye Tunga Rogo Dutsin Nasarawa, ya ce mutum 26 aka kashe a yammacin ranar Laraba, ba tare da samun dauki daga jami’an tsaro ba.
Ya ce ’yan bindigar sun kuma hana daukar gawarwakin mutanen da suka kashe don yi musu sutura kamar yadda addinin musulumci ya tanadar.
Kokarin jin ta bakin kakakin ’yan sandan jihar Zamfara, SP Shehu Mohammed ya ci tura.
A baya-bayan nan Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Mohammed Matawalle, ya sha alwashin saka kafar wando daya da ’yan bindigar da suka dade suna addabar jihar.