Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun kai hare-hare a kauyukan da ke jihar Zamfara inda suka kashe mutum 23 tare da kone gidaje da rumbunan abinci.
’Yan bindigar sun kai wa kauyukan da suka hada da kauyen Barka da Yabo da Mallamawa da Tungar Kahau da Maikamarrimi da Gidan Anna da ke karamar hukumar Shinkafi hari da tsakar rana.
Gungun maharani sun kai harin ne a kan babura inda suka bude wuta a kan mazauna garin tare da kone gidaje sannan suka kone kayayyakin abincin mutanen garin bayan sun gudu.