✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kashe mutum 2, sun sace manoma 10 a Neja

Rahotanni sun bayyana cewar har da ɗan sa-kai daga cikin waɗanda suka rasa rayukansu a harin.

’Yan bindiga sun kashe mutum biyu tare da yin awon gaba da aƙalla wasu 10 a hare-haren da suka kai Ƙananan Hukumomin Wushishi da Rafi a Jihar Neja.

Wani jami’in tsaro da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa Aminiya cewa waɗanda aka kashe sun haɗa da ɗan sa-kai da wani mutum mai saran itace.

Har ila yau, ya ce wani ɗan sa-kai na daga cikin waɗanda aka sace.

“A halin yanzu, ’yan bindiga suna cikin dajin Akare. Sun sace ɗaya daga cikin ‘yan sa-kai, kuma yana da bindigogi biyu a tare da shi lokacin da suka yi awon gaba da shi.

“Ba mu san abin da za mu yi a yanzu ba. Mun shafe tsawon ranar ɗaya muna fafatawa da su. An kashe ɗaya daga cikin ’yan sa-kai da kuma wani mai saran itace,” in ji shi.

Mazauna yankin sun bayyana cewa har kawo hanzu ’yan bindigar suna cikin dajin tare da shanun da suka sace a yankin.

An ruwaito cewa sun kama mai saran itacen, tare da tilasta masa ya nuna musu hanya, sannan suka harbe shi.

Wasu majiyoyi sun bayyana cewa jami’an tsaro da ’yan sa-kai na ci gaba da ƙoƙarin bin sahun ‘yan bindigar.

Wani mazaunin yankin ya ce, “Mun ga ’yan bindigar suna tafiya da babura, uku-uku a kan kowanne.

“Suna wucewa ta wajen da suka saba bi a Kundu, a Ƙaramar Hukumar Rafi, sun nufin Ƙaramar Hukumar Mashegu tare da shanun da suka sace.”

Wani mazaunin Ƙaramar Hukumar Rafi, ya ce ’yan bindigar sun kuma kai hari wasu ƙauyuka a gundumar Gunna da safiyar ranar Laraba, inda suka ƙone rumbunan doya.

Da yake tabbatar da harin, Kwamishinan Tsaron Cikin Gida na Jihar Neja, Birgediya Janar Bello Abdullahi Mohammed (mai ritaya), ya ce, an tura ƙarin jami’an tsaro zuwa yankin.

“An riga an tura jami’an tsaro zuwa yankin, kuma suna bin sahun ’yan bindigar.”