✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘Yan bindiga sun kashe mutum 2, sun sace 4 a Sakkwato

Maharan sun kashe mutum biyu yayin da suke tsaka da aiki a gonakinsu.

Rahotanni da ke fitowa daga Jihar Sakkwato sun bayyana cewar wasu ‘yan bindiga sun hallaka mutum biyu yayin da suke tsaka da aiki a gonakinsu a Karamar Hukumar Sabon Birni da ke Jihar.

Aminiya ta ruwaito cewa lamarin ya faru da misalin karfe 3:30 ma Yammacin ranar Lahadi.

Shugaban ‘yan bangar garin Sabon Birni, Musa Muhammad (Blacky), ya bayyana sunayen wanda aka kashe; Hamza Na’Allah da Zubairu Haruna.

Blacky ya kara da cewar mutum uku maharan suka farmaka yayin da suke aiki a gonarkin nasu, amma daya daga cikinsu ya yi nasarar tserewa zuwa wani kauye da ke kusa da su.

Sai dai ya ce duk da fara samun wanzuwar zaman lafiya a yankin, duk da haka ana samun kananan hare-hare daga ‘yan bindiga lokaci zuwa lokaci.

A cewarsa, kwanaki hudu da suka wuce wasu mahara sun sace mutum hudu a kan hanyar Sabon Birnin zuwa Goronyo.

Mun yi kokarin jin ta bakin kakakin ‘yan sandan jihar, ASP Sanusi Abubakar kan faruwar lamarin, amma ba mu samu damar ganawa da shi da ba zuwa wannan lokaci.