A yammacin ranar Litinin wasu ’yan bindiga a kan babura suka kai hari kauyen Tsauwa da ke Karamar Hukumar Batsari ta Jihar Katsina, inda suka kashe mutum 19.
A cewar wata majiya sun kai harin ne da misalin karfe 5:45 na yamma, inda suka tarwatsa mutanen kauyen sannan suka kashe 19 daga ciki.
- Matashi ya datse wa tsohuwa kai a Kalaba
- Bidiyon Dala: Kotu ta umarci Ganduje ya biya Jaafar Jaafar N800,000
Majiyar ta kuma tabbatar da cewar ’yan bindigar sun kone gidaje da dama tare yin awon gaba da shanu da kananan dabobbi.
Kazalika, wata majiyar a yankin ta shaidawa wakilin Aminiya cewar sai da mazauna yankin suka sanar da jami’an tsaro ana tsaka da kai harin amma babu wanda ya kau musu dauki.
“Bayan ficewarsu daga kauyen, sun wuce zuwa kauyen ’Yar Lumo inda suka kwana suna kida suna harba bindigar murnar nasarar da suka yi a Tsauwa.
“An tabbatar da mutuwar mutum 19, sannan da yawa sun bata, babu tabbacin ko suna raye,” cewar majiyar.
Kazalika, majiyar ta ce wani mazaunin kauyen da ya kira wayar dan uwansa don jin halin da yake ciki sai wani dan bindiga ya amsa, inda ya ce masa “Kun kashe mana mutum biyu, mu ma mun rama.”
Tuni dai aka binne mutanen da suka rasu a ranar Talata kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.
Idan ba a manta ba, ko a ranar 17 ga Fabrairun 2020, sai da ’yan bindigar suka kai farmaki kauyen na Tsauwa inda suka kashe mutum 21.
Da aka tuntubi kakakin ’yan sandan Jihar, SP Gambo Isah, ya tabbatar da faruwar harin, inda ya ce mutum 18 aka kashe, aka raunata mutum daya sannan mutum daya ya bace.
“Kwamishanan ’yan sanda Sanusi Buba, ya ziyarci kauyen da kansa inda ya umarci a bankado maboyar ’yan bindigar tare da gurfanar da su gaban kotu.”