✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun kashe mutum 18 suna sallah a masallaci a Neja

An kai hari masallacin ne lokacin da mutane ke sallar Asuba.

Akalla mutum 18 ne aka tabbatar da rasuwarsu bayan wani hari da ’yan bindiga suka kai wani masallaci a kauyen Maza-Kuka a Karamar Hukumar Mashegu ta Jihar Neja.

Majiyoyi sun shaida wa wakilinmu cewa maharan masu tarin yawa sun yi wa kauyen kawanya ne a kan babura sannan suka wuce kai tsaye zuwa masallacin, yayin da mutanen ke sallar Asuba, suka kashe 18 daga cikinsu.

A cewar wasu majiyoyi da suka nemi a sakaya sunansu, maharan sun kuma jikkata wasu masu ibadar da dama a masallacin, sannan suka sace wasu mutum 13.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar, ta bakin Kwamishinanta, Mista Monday Kuryas, ta tabbatar da faruwar harin a ranar Litinin.

Kuryas ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 5:30 na Asuba, sai dai ya ce maharan sun yi garkuwa da mutum bakwai ne.

Kwamishinan ya kuma ce maharan sun lalata kadarori na miliyoyin Nairori, amma ya ce jami’an tsaro sun yi nasarar kashe daya daga cikinsu yayin harin.

Kwamishinan ya kuma ce suna zargin harin wani yunkuri ne na daukar fansa daga ’yan bindigar.

Ya ce tuni aka aike da karin jami’an tsaro kauyen don tabbatar da tsaro da kuma maganin tsagerun da ke kokarin kawo wa zaman lafiya tarnaki.

Kazalika, ya karfafi gwiwar jama’a, musamman mazauna karkara da su ci gaba bayar da bayanan sirri da za su taimaki jami’an tsaro wajen cafke bata-gari tare da gurfanar da su gaban kuliya.

%d bloggers like this: