✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘Yan bindiga sun kashe mutum 17 a Benuwai

Akalla mutane 17 ne suka rasa rayukansu yayin da ’yan bindiga suka kai hari wasu yankuna a Karamar Hukumar Gwer ta Yamma a Jihar Benuwai.…

Akalla mutane 17 ne suka rasa rayukansu yayin da ’yan bindiga suka kai hari wasu yankuna a Karamar Hukumar Gwer ta Yamma a Jihar Benuwai.

Wakilinmu ya rawaito cewa, ’yan bindigar sun kai sabon harin da safiyar ranar Litinin.

Mazauna sun ce ’yan bindigar sun kashe kimanin mutane 17 a yankunan biyu da suka kai hari.

Wasu da abun ya faru a kan idonsu, sun ce mutane da dama sun tsere bayan ’yan bindigar sun cinnawa gidaje da dama wuta.

Wani mazaunin kauyen ya bayyana cewa, akwai yiwuwar adadin wadanda suka rasa rayukansu ya karu inda a halin yanzu an nemi mutane da dama an rasa bayan aukuwar harin.

Yayin da aka tuntubi Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar, DSP Catherine Anene, ya ce sun samu labarin aukuwar harin sai dai basu da cikakken bayani a kansa.