✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kashe mutum 15 a Sallar Asuba a Neja

Sun bude wa mutanen wuta a yayin da suke tsaka da sallah, wata biyu bayan irin harin a wani masallaci

Mutum 15 sun rasu bayan ’yan bindiga sun bude musu wuta a lokacin da suke tsaka da Sallar Asuba a masallaci a kauyen Ba’are da ke Karamar Hukumar Mashegu ta Jihar Neja.

Majiyarmu a yankin ta ce maharan sun kuma jikkata mutane dama, wadanda aka garzaya da su zuwa Babban Asibitin Kontagora domin kulawa da su.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Neja, Monday Bala Kuryas, ya tabbatar da harin, amma ya ce, “Rundunar ’Yan Sandan Jihar Neja ta tura jami’an tsaro domin kare rayuka da dukiyoyi a yankin.”

A cewarsa, mutum tara ne aka kashe a harin, sabanin adadin da jama’ar garin suka shaida mana.

Kwamishinan ’Yan Sandan ya ya kuma ba wa jama’a tabbacin samun cikakkiyar kariya daga jami’an tsaro, yana mai rokon su da su rika taimakawa da bayanan sirri.

Kimanin wata biyu ke nan da wasu mahara suka hallaka mutum 18 a lokacin da suke Sallar Asubahi a wani masallaci a kauyen Mazakuka a Karamar Hukumar ta Mashegu.