Kimanin mutum 15 ne ake fargabar sun mutu a wani hari na ranar Lahadi da ’yan bindiga suka kai Kananan Hukumomi Goronyo da Illela na Jihar Sakkwato.
Gwamnan Jihar, Aminu Waziri Tambuwal wanda ya tabbatar da hakan a ranar Litinin, ya ce mutum 12 aka kashe a Illela yayin da kuma ragowar ukun suka rasa rayukansu a Goronyo.
- Budurwar da ta jira saurayinta shekara 16 ya fito a gidan yari
- Ko Kwankwaso da Shekarau sun hade ba za su gagare mu ba – Zaura
Gwamna Tambuwal ya bayyana haka ne jim kadan gabanin gabatar da Kasafin Kudin Jihar Sakkwato na shekarar 2022 a gaban Majalisar Dokokin jihar.
Tambuwal hare-haren sun auku ne a tsakanin daren Lahadi zuwa wayewar gari na Litinin a Kananan Hukumomin da lamarin ya shafa.
Gwamnan ya kuma mika ta’aziyyarsa ga ’yan uwan wadanda suka mutu da kuma wadanda suka jikkata a hare-haren.
Bayanai sun ce Kananan Hukumomin biyu da lamarin ya shafa na daga cikin wadanda gwamnati ta bayar da umarnin katse musu layukan sadarwa a yunkurinta na kawo karshen matsalar tsaro a Jihar.
Duk wannan dai na faruwa ne a yayin da wasu rahotanni ke cewa yan bindiga sun fara daula a kauyuka da dama na Jihar Sakkwato inda har sun shata wa mazauna haraji.