Wasu ’yan bindiga sun halaka mutum 15 a kauyan Gonar Rogo a gundumar Kufana da ke karamar hukumar Kajuru a jihar Kaduna.
Lamarin ya faru ne da misalin karfe 11:30 na daren Litinin.
Maharar sun sace shanu tara sannan suka raunata wasu, a yanzu haka wadanda suka samu rauni suna jinya.
Rahotonni daga yankin sun ce, akalla mutum 15 ne suka rasu wasu kuma sun jikkata. Maharar sun kwashe shanu tara kafin su fice daga cikin kauyan.
- Harin ‘yan bindiga ya tilastawa makiyaya 350 yin hijira a Neja
- An yi garkuwa da matar aure da kanwarta a Kaduna
Shugaban karamar hukumar da Hakimin Kufana da sauran jami’an tsaro sun ziyarci yankin.
Buhari ya yi Allah wadai da harin Kajuru
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi tir da abin da ya bayyana “hare-haren ramuwar gayya a yankin karamar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna.
Shugaban ya bayyana hakan ne a wani sakon tiwita da ya wallafa cikin daren ranar Talata, inda ya ce ba daidai ba ne kisan gilla da sunan ramuwar gayya.
Buhari ya yi Allah wadai game da hare-haren ramuwar gayya tsakanin kabilun yankunan Kajuru.
PRESIDENT BUHARI CONDEMNS KILLINGS IN THE NAME OF REVENGE
President @MBuhari has again condemned the wave of attacks and counterattacks on people among the Fulani and Addara communities in Kajuru LGA of Kaduna State, saying that killing in the name of revenge is wrong.
— Presidency Nigeria (@NGRPresident) May 12, 2020