✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun kashe mutum 13 a Katsina

'Yan bindigar sun kai harin don daukar fansar kwace shanu da wasu matasa suka yi a hannunsu.

’Yan bindiga sun kai hari a garin Sabuwa na Karamar Hukumar Sabuwa, Jihar Katsina, inda suka kashe mutum 13 tare da raunata wasu.

Wani mazaunin garin ya shaida wa wakilinmu cewa harin ramuwar gayya ce bayan kwace shanu da ’yan bindigar suka yi daga hannun wasu matasa da ke dibar yashi da su amma matasan suka kwato shanun.

“Bayan kwace shanun daga hannun matasan, sai samarin suka gayyato abokansu suka kwato su daga hannun ’yan bindigar.

“Hakan ne ya sa ’yan bindigar suka gayyato abokansu sama da 100 suka rika harbin duk wanda suka gani a kauyen,” inji shi.

Rahotanni sun bayyana cewa an kai harin ne da misalin karfe 5:30 na yammacin ranar Talata.

An binne mutum biyu a ranar Talata, sai kuma mutum 11 da aka yi wa sallah a Masallacin Juma’ar garin ranar Laraba.

Aminiya ta kuma samu rahoto cewa ’yan bindiga sun kashe wani mutum mai suna Haruna Tsaunin Batsi tare da raunata wasu biyu a Tsaunin Batsi da ke yankin Sayau a Karamar Hukumar ta Sabuwa.

Wani mazaunin kauyen ya shaida wa wakilinmu cewa ’yan bindigar sun shiga kauyukan Tsaunin Batsi da Dankurmi ne da misalin karfe 2 na daren ranar Talata, amma ba su yi garkuwa da kowa ba.

Mutumin ya yi roko da a kawo jami’an tsaro kauyen Tashar Bawa, inda ya ce ta nan ne ’yan bindigar ke shigo musu.