✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun kashe mutum 1, sun sace mata 16 a Neja

Maharan sun yi awon gaba da wasu mata hudu da ke shayarwa.

Wasu ‘yan bindiga sun kashe mutum daya tare da yin garkuwa da mata 16, ciki har da masu shayarwa hudu a unguwar Hayin-Magaji da ke Karamar Hukumar Kontagora ta Jihar Neja.

Aminiya ta gano ‘yan bindigar da suka kai harin sun yi wa yankin da ke da tazarar kilomita kadan daga garin Kontagora, hedkwatar Karamar Hukumar Kontagora tsinke, inda suka ci karensu ba babbaka da misalin karfe 2:00 na daren Litinin.

Wani mazaunin unguwar da ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce mutane da dama sun samu raunuka kuma tuni aka mika su Babban Asibitin Kontagora don samun kulawa.

Ya ce wasu mazauna yankin da dama kuma sun tsere daga gidajensu saboda harin, ya kuma yi kira ga gwamnati da ta kawo musu dauki domin dakile rashin tsaron da ya addabi yankin.

“Jarirai hudu ne tare da iyayensu aka yi awon gaban da su saboda iyayensu mata ba za su iya barin su ba, kauyenmu ba shi da nisa da Farin-Shinge, mai tazarar kilomita kadan daga Kontagora, mutane da dama suna kwance a asibiti a halin yanzu. Allah ne kadai Ya san ko za su rayu”.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, mun kasa jin ta bakin Kakakin Rundunar ‘yan sandan Jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun ko kuma ta bakin Kwamishinan Tsaron Cikin Gida da Jin Kai na jihar, Emmanuel Umar.

Jihar Neja dai na daya daga cikin jihohin Arewa da ‘yan fashin daji da masu garkuwa da mutane suka addabi.