✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun kashe mutane da dama a sansanin sojoji a Sakkwato

Majiyoyi sun ce an kai harin ne da sanyin safiyar ranar Juma’a.

Wasu ’yan bindiga sun kai hari sansanin sojoji na hadin gwiwa da ke Karamar Hukumar Sabon Birni a Jihar Sakkwato sannan suka kashe mutane da dama.

Wakilinmu ya gano cewa ana yi wa sansanin wanda ke kauyen Dama lakabi da sansanin Burkusuma.

Majiyoyi sun ce an kai harin ne da sanyin safiyar ranar Juma’a.

Tsohon Shugaban Karamar Hukumar ta Sabon Birni, Idris Muhammad Gobir, wanda ak fi sani da Dancadi, shi ne ya tabbatar da rahoton kai harin inda ya ce jami’an tsaro da dama kuma sun yi batan-dabo.

Kazalika, ya ce maharan sun kona wata motar sintiri ta sojojin sannan suka gudu da wata wacce suka yi amfani da ita wajen sufurin kayan abincin da suka sata daga kauyen.

Da wakilinmu ya tuntubi kakakin ’yan sanda na Jihar, ya ce sun sami rahoton kai harin daga wani mazaunin yankin wanda ya kira su da wayar salular Jamhuriyar Nijar.

“Amma zan sake tuntubar shi don samun cikakkun bayanai, alabasshi daga bisani in yi maka bayani,” inji shi.

To sai dai wani fitaccen mazaunin yankin ya tabbatar da cewa an turo wasu motoci domin debe gawarwakin jami’an tsaron da aka karkashe a harin.

“Yanzu haka kuma akwai kimanin motoci 10 cike da jami’an tsaro da suka shiga dazukan yankin don bin sahun ’yan bindigar,” inji majiyar.

Kazalika, shi ma wani jami’in hukumar tsaro ta NSCDC wanda ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar wa wakilinmu cewa akwai jami’ansu uku daga cikin wadanda aka kashe a yayin harin.

“Maganar da nake yi da kai yanzu haka muna dakin adana gawarwaki don mu kwashe su mu je mu yi musu jana’iza,” inji shi.

Rahotanni sun kuma tabbatar da cewa ’yan bindigar sun kai hari garin Katsira inda suka harbe mutum hudu sannan suka tafi da wasu mutum uku.

Biyu daga cikin wadanda aka kashe din sun mutu ne nan take, ragowar kuma suna wani asibiti suna samun kulawa.