A jihar Neja, akalla mutane 10 ne ’yan bindiga suka hallaka, wasu 24 kuma aka yi garkuwa das u bayan wani hari da suka kai wasu yankunan jihar.
Rahotanni daga kauyukan da lamarin ya shafa na cewa biyar daga cikin mutanen da aka halaka maza ne ’yan kungiyar agaji, ragowar kuma yara ne masu taimakwa ’yan agajin yayin da suke gudanar da sintiri.
- Yadda tsoma bakin uwar miji ya yi sanadiyyar mutuwar aure
- ‘Yan majalisar tarayya 2 na PRP da APGA sun sauya sheka zuwa APC
- ’Yan Najeriya da suka zama zakaran gwajin-dafi a Duniya
Wasu majiyoyi daga yankin sun ce ’yan bindigar sun kai harinne da misalin karfe 12:30 na rana, inda suka yi ta cin karansu ba babbaka har zuwa wurin karfe 2:00 na rana.
Gwamnatin Jihar ta Neja dai ta tabbatar da kashe Dagacin kauyen Kusherki da ke Karamar Hukumar Rafi, Alhaji Masud Abubakar, inda kuma ’yan bindigar kuma suka yi awon gaba da mai dakinsa.
Rahotanni sun ce yawan maharani, wadanda ywansu ya kai akalla 50, sun yi wa kauyukan tsinke, dukkansu a kan babura dauke da muggan makamai da suka hada da bindiga kirar AK-47.
Wasu mazauna yankin sun ce ’yan bindigar sun fara ta’asar ne daga kauyen Kasuwe sannan suka shiga sauran kauyukan inda suka rika afkawa mutanen kauyen suka ci gaba da karkashe su baji ba gani.
Kazalika, ’yan bindigar sun kuma tarwatsa kayan abincin mutane tare da lalata wasu kayayyakinsu masu muhimmanci.