✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun kashe mata da yara kusan 20 ana tsaka da sallar Juma’a a kauyukan Zamfara

Rahotanni sun ce an kai harin ne lokacin da mazauna yankin ke gudanar da sallar Juma’a.

Wasu ’yan bindiga sun kashe akalla mutum 20, yawancinsu mata da kananan yara a Kananan Hukumomin Bungudu da Tsafe da ke Jihar Zamfara.

Mazauna yankin sun ce a harin da aka kai kauyen ’Yar Katsina da ke Karamar Hukumar Bungudu, an kashe akalla mutum 10.

’Yan ta’addan, wadanda yawansu ya kai kusan 100 sun kai harin ne a kan babura sannan suka sace wasu mutanen, a daidai lokacin da mazauna yankin ke gudanar da sallar Juma’a.

Wani ganau ya shaida wa wakilinmu cewa, “Sun zo da yawan gaske a kan babura sannan suka bude wa mutane wuta. ’Yan Sa-kai sun taka rawar gani matuka wajen kai dauki, in ban da haka, da yawan wadanda aka kashe ma ya fi hakan.

“Mafi yawan wadanda aka kashe mata ne da kananan yara, kuma su ma maharan an kashe musu mutane,” inji shi.

Shi ma wani mazaunin garin Magami mai suna Babangida, ya shaida wa Aminiya cewa an hangi maharan na kokarin yin hanyar garin Dandundun da mutanen da suka sace.

A wani labarin makamancin wannan, maharan sun kuma kai hari Garin Nasarawa Mai Fara da ke Karamar Hukumar Tsafe, inda nan ma suka kashe mutum 10.

Mazauna yankin sun ce an kai musu harin ne bayan da suka gaza biyan harajin da ’yan bindigar suka yanka musu.

Kokarin wakilinmu na jin ta bakin Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, SP Muhammad Shehu, kan lamarin ya ci tura.