✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun kashe mai gari da mutum biyar a Zamfara

Jami’an tsaro tare da hadin gwiwar ’yan sa-kai an yi wa ’yan bindigar tara-tara.

’Yan bindiga sun kashe mai garin Gada a Karamar Hukumar Maru ta Jihar Zamfara tare da wasu mutum biyar.

Aminiya ta ruwaito cewa, ’yan bindigar sun harbe Alhaji Umaru Bawan Allah yayin da suka afka wa garin na Gada a ranar Laraba.

Mazauna sun ce gomman ’yan bindigar sun afka wa gidaje inda suka rika yi wa mutanen dauki dai-dai suna harbe su.

Bayanai sun ce ’yan bindigar sun kuma yi awon gaba da wani adadi na mutane ciki har da mata da yara wadanda suka yi kokarin arcewa domin neman tsira.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, jami’an tsaro tare da hadin gwiwar ’yan sa-kai an yi wa ’yan bindigar tara-tara da har aka samu nasarar ceto mutanen da suka diba.

Wani mazaunin yankin mai suna Aliyu, ya ce an ci karfin ’yan bindigar ne yayin musayar wuta, lamarin da ya sanya suka arce suka bar mutanen da suka sata.

Sai dai har ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, neman jin ta bakin Mai Magana da Yawun ’Yan Sandan Jihar Zamfara, SP Muhammad Shehu ya ci tura.

%d bloggers like this: