✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kashe mai gadi a gidan tsohon minista

Maharan sun bude wuta a gidan tsohon Ministan Wasanni Damishi Sango

’Yan bindiga sun kai hari a gidan tsohon Ministan Wasanni Damishi Sango da ke Ganawuri, Karamar Hukumar Riyom a Jihar Filato.

Maharan sun yi wa mutum biyu ruwan wuta, cikinsu har da mai gadi, a lokacin da suka yi wa gidan dirar mikiya ranar Laraba da dare.

An garzaya da mutanen da aka harba din zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos (JUTH) amma ran mai gadin ya yi halinsa.

Kakakin ’yan sanda a Jihar Filato, Gabriel Ubah, ya tabbatar da labarin amma ya ce, “An tura jami’an binciken kwakwaf su bi sawu tare da kamo bata-garin.”

Ya ce Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Filato, Edward Egbuka, ya ziyarci gidan tsohon ministan kan abin da ya faru.

Babu bayani game da ko Damishi Sando da iyalansa na cikin gidan a lokacin da aka kai harin.

Damishi Sango shi ne tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP na Jihar Filato.