Wasu ‘yan bindiga sun kashe babban limamin masallacin Juma’a na kauyen Keita da ke Karamar Hukumar Tsafe a Jihar Zamfara, Sheikh Ahmad Rufa’i.
Kisan Sheikh Rufa’i ya zo ne bayan makonni uku da kashe Imam Abubakar Hassan Mada, babban masallacin Mada da ke Karamar Hukumar Gusau ta jihar.
Wani mazaunin Keita, Ibrahim Musa Keita, ya ce ‘yan bindigar sun yi wa ƙauyen ƙawanya ne jim kaɗan bayan da jama’a sun shiga sallar isha’i.
Ya yi bayanin cewa, “Kafin mamayar, an sanar da mazauna garin game da shirin farmakin ‘yan bindigar a kan titin Kwarin Gano zuwa Keita. An hango su a kan hanyar amma ba mu da tabbacin ko za su zo wannan ƙauyen ko sabanin haka.
“Da farko sun so su yi awon gaba da matafiya a kan hanyar Keita zuwa Ƙwarin Gano, amma bayan sun ɗauki lokaci ba tare da samun ko mutum ɗaya ba, sai suka mamaye ƙauyen Keita, suka kashe babban limaminmu tare da sace mutane da dama ciki har da mata.
“Ba mu tantance adadin mutanen da suka yi garkuwa da su ba yayin da akwai wadanda suka sun tsere cikin daji har yanzu ba a gansu ba.”
A wani labarin mai nasaba da wannan, an yi garkuwa da mutane biyu a ƙauyen Magazu da ke Karamar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamafaran a ranar Talata.
Wani mazaunin garin mai suna Yusuf Ibrahim ya ce ‘yan bindigar sun kai farmaki ƙauyen ne da misalin ƙarfe uku na safe, inda suka riƙa harbe-harbe.
Ya ƙara da cewa galibin mazauna garin sun tsere daga gidajensu.
Har ila yau, wani mazaunin ƙauyen Kwalfada da ke maƙwabtaka da su, mai suna Aminu Kwalfada, ya bayyana takaicin yadda ayyukan ‘yan ta’addan ya tilasta wa mazauna garin daina amfani da lasifika a cikin masallatan su a lokutan sallah.
Aminiya ta yi kokarin jin ta bakin jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan Jihar Zamfara, ASP Abubakar Yazid, wanda ya yi alƙawarin cewa zai bayar da bayanai dangane da lamarin da zarar ya samu cikakken rahoto, amma har zuwa lokacin hada wannan rahoto bai yi bayani ba.