Wasu ’yan bindiga sun kashe wani magidanci mai suna Ken Ekwesianya da matarsa da diyarsu a Karamar Hukumar Ihiala ta Jihar Anambra.
Wata majiya ta bayyana cewa an kashe iyalan ne yayin da suka je ibada a coci a daren Juma’a.
- Raddin Sheik Abduljabbar ga Ganduje
- An kama makauniyar karya a Anambra
- Gobara ta lakume shaguna a kasuwar Anambra
- ‘Yan bindiga sun kashe mutum 2 a Kaduna
Kakakin ’yan sandan jihar, Haruna Mohammed, ya tabbatar da aukuwar lamarin, sai dai bai yi cikakken bayani game da abin daya faru ba.
Muhammad ya kara da cewa, Rundunar ’Yan Sandan jihar ta kafa dambar bincike don gano wadanda suka aikata laifi.
Ya ce da zarar sun samu wani bayani ko kama wanda suka aikata laifin za su sanar da manema labarai.