✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun kashe jami’in kwastam bayan karbar kudin fansa

Sun kashe shi bayan karbar miliyan daya a hannun ’yan uwansa.

’Yan bindiga sun kashe wani mutum da suka yi garkuwa da shi bayan sun karbi kudin fansa Naira miliyan daya daga hannun ’yan uwansa.

A watan Fabrairu Aminiya ta rawaito yadda wasu ’yan bindiga suka kai hari a unguwar Rigachikun da ke Karamar Hukumar Igabi ta Jihar Kaduna, inda suka sace mutane da dama ciki; har da wata amarya da aka kusa bikinta.

A yayin harin, ’yan bindigar sun harbi wani jami’in hukumar kwastam wanda daga bisani ya rasu a asibiti.

Wata mata a yankin ta shaida wa Aminiya cewa an samu labarin rasuwar mutumin bayan ’yan uwansa sun kai kudin fansa ga ’yan bindigar.

“Sun harbe shi bayan an kai musu kudin da suka bukata. Gaba daya mutanen yankin nan sun shiga damuwa bayan samun labarin mutuwarsa,” a cewarta.

Aminiya ta gano an yi jana’izar mamacin a Unguwar Shanu inda ’yan uwansa ke da zama.

Kazalika, rahotanni sun bayyana cewa har yanzu amaryar da aka kusa bikinta da wani mutum suna can a hannun ’yan bindigar.