✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun kashe jami’an tsaro uku a Kaduna

’Yan bindiga sun kashe jami’an Hukumar ’Yan Sintiri ta Jihar Kaduna (KADVIS) uku a Karamar Hukumar Chikun ta jihar. An bindige jami’an ne a kauyen…

’Yan bindiga sun kashe jami’an Hukumar ’Yan Sintiri ta Jihar Kaduna (KADVIS) uku a Karamar Hukumar Chikun ta jihar.

An bindige jami’an ne a kauyen Dende a hanyarsu ta dawowa daga  Damba-Kasaya da ke Buruku.

“Suna dawowa ne unguwar lokacin da aka kai musu hari aka kashe mutum uku daga cikinsu”, inji Mista Luka Barde, mazaunin unguwar.

Ya tabbatar wa wakilin Aminiya cewa lamarin ya auku ne a daren Laraba.

Kwamishinan TSaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar, Samuel Aruwan ya tabbatar da aukuwar lamarin a cikin wata sanarwa.

Ya ce mamatan su hada da Alison Musa, Dauda Audu da kuma Ishaya Sarki, akwai kuma Ayuba Tanko Doza Adamu da ke kabar magani sakamakon raunukan da suka samu.