’Yan bndiga sun kashe wani jagoran al’umma kana sun sace matan aure hudu ciki har da mai shayarwa a kauyen Unguwar Mai Awo a Jihar Kaduna.
Majiyarmu ta ce da safiyar Laraba maharan suka shiga kauyen wanda ke kusa da Maraban Jos a babbar hanyar Kaduna zuwa Zariya.
- Maigidanci ya nemi matarsa ta biya shi N320,000 a madadin aurensu
- Da gangan aka kirkiri Boko Haram don a wargaza Najeriya – Buhari
Shugaban matasan yankin, Adam Unguwar Awo, ya tabbatar wa Aminiya da aukuwar hakan.
Adam ya ce bayan shigarsu kauyen, maharan sun yi harbe-harben bindiga a iska don razana jama’a.
A cewarsa, “’Yan bindigar sun kashe Malam Ibrahim Abdullahi wanda jagora ne, kuma Shugaban Kungiyar Agaji ta Fityanul Islam na yankin, hade da wani yaron dan uwansa, Zakari Yau.
“Sannan sun sace matan aure hudu, ciki har da wata mai shayarwa,” in ji shi.
Da aka nemi jin ta bakinsa kan batun, Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ‘Yan Sandan Jihar, DSP Mohammed Jalige, ya ce zai bincika sannan ya yi bayani amma zuwa hada wannan rahoto babu motsinsa.