’Yan bindiga sun kashe wani fasto, Rabaran Bala Galadima yayin harin da suka kai garin Lubo da ke Ƙaramar Hukumar Yamaltu Deba a Jihar Gombe.
Aminiya ta ruwaito cewa, ’yan bindigar sun kuma yi fashin kuɗi har Naira dubu 300 a yayin harin da suka kai cikin dare wayewar gari Lahadi.
Wani mazaunin garin ya bayyana cewa maharan, waɗanda sun kai takwas, sun kai farmakin ne da misalin karfe 1 zuwa 3 na dare, inda suka firgita jama’a da harbe-harbe kafin su kutsa cikin gidan wani mutum mai suna Musa Puma.
Majiyar ta ce maharan sun rutsa matar gidan da bindiga inda suka karbi kuɗi naira dubu dari 300 tare da yin garkuwa da ɗaya daga cikin ’ya’yansu da kuma barazanar kashe shi muddin aka yi musu tirjiya.
Shi kuwa Faston Cocin ECWA na garin Lubo, Rabaren Bala Galadima, ya rasa ransa ne bayan da maharan suka harbe shi a gadon baya a gidansa, lamarin da ya girgiza al’ummar garin.
Gwamnati Ta Yi Allah Wadai
Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, ya yi Allah wadai da kisan Rabaren Bala Galadima, tare da bayyana alhininsa kan wannan aika-aika.
A wata sanarwa da Babban Daraktan Yada Labarai na Gwamnatin Jihar, Isma’illa Uba Misilli ya fitar a ranar Litinin, gwamnan ya bayyana kisan a matsayin zagon kasa ga zaman lafiya da tsaron Jihar Gombe.
“Wannan kisan Fasto Rabaren Bala Galadima babban abin takaici ne. Babu shakka, wannan aiki zagon ƙasa ne ga zaman lafiya da tsaro wanda Jihar Gombe ta shahara da shi.
“Ba za mu lamunci irin waɗannan abubuwa da ke kawo cikas ga zaman lafiya a jiharmu ba,” in ji Gwamna Yahaya.
Gwamnan ya kuma umurci hukumomin tsaro da su zakulo waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aiki tare da gurfanar da su a gaban kotu.
Ya yi kira ga jama’a da su ci gaba da bayar da goyon baya ga hukumomin tsaro domin tabbatar da cewa irin wannan lamari bai sake faruwa ba.
Gwamnati ta kuma yi kira ga al’ummar jihar da su kasance masu kula da tsaron kansu tare da sanar da hukumomin tsaro duk wani motsi da suke zargin zai iya kawo barazana ga zaman lafiya.
Gwamnan ya ba da tabbacin cewa ba za su yi ƙasa a gwiwa ba wajen ganin an kawo ƙarshen ayyukan ta’addanci a jihar.
A nasu ɓangaren, rundunar ’yan sandan Gombe ta bakin mai magana da yawunta, DSP Buhari Abdullahi ta ce tuni aka aike da jami’ai domin gudanar da bincike kuma nan gaba kaɗan za su fitar da jawabi.