✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun kashe DPO da jami’ansa takwas a Kebbi

Rahotanni daga Jihar Kebbi da ke Arewa maso Yammacin Najeriya sun tabbatar da cewa ’yan bindiga sun kashe wani DPO da jami’ansa yayin da kai…

Rahotanni daga Jihar Kebbi da ke Arewa maso Yammacin Najeriya sun tabbatar da cewa ’yan bindiga sun kashe wani DPO da jami’ansa yayin da kai dauki wani kauye da aka kai hari.

Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar, ASP Nafi’u Abubakar ne ya tabbar da hakan yayin ganawarsa da sashen Hausa na BBC a ranar Lahadi.

“Da misalin karfe 2.30 na rana ne DPO na Kasa ya samu labarin ’yan bindiga sun kai hari kauyen Makuku da wasu kauyukan da ke kewaye da shi.

“Nan da nan da ya jagoranci yaransa su takwas da zummar kai dauki inda yayin fatawa da maharan kwanansu ya kare,” in ji ASP Nafi’u.

An ruwaito cewa Sanata Bala Ibn Na’Allah da ke wakiltar yankin ne ya nemi taimakon rundunar sojin sama, inda kaa tura jirgin yaki ya fatattaki ’yan bindigar daga kauyukan.

A Talatar da ta gabata ce wasu ’yan bindiga suka kai hari kauykan Kunduru, Bajida, da Rafin Gora in da suka yi awon gaba da shanu da dama.

Yanzu haka dai mazauna kauyukan sun fara tattara ina su ina su suna barin matsugunansu domin tsira da rayukansu.