✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun kashe dan sanda sun kona caji ofis a Binuwai

An yi dauki ba dadi tsakaninsu da jami'an tsaro kafin su ranta a na kare.

’Yan bindiga harbe wani hafsan dan sanda suka kuma kona gidaje da dama ciki har da ofishin ’yan sanda a unguwar Tse Harga da ka Karamar Hukumar Katsina-Ala a Jihar Binuwai.

Shugaban Karamar Hukumar Katsina-Ala, Alfred Atera, ya tabbatar da aukuwar harin a yankin wanda ya ce matsalar tsaro ta sa matasa kafa kungiyar sintiri kuma suna kokari wajen yakar matsalar..

‘‘Sun auka wa matasan da ke aikin sintiri a yankin, suka kona ofishin ’yan sanda, motar sintirin ’yan sanda suka kuma kashe wani dan sanda a wurin.

‘‘Sun kuma kona gidaje da dama wadanda ba zan iya tantance su ba yanzu. Amma game da mazauna yankin, ba wanda aka kashe,’’ inji shi.

Aminiya ta gano cewa maharan sun yi wa yankin dirar mikiya ne da misalin karfe hudu na asubahin Alhamis suna harbi ba kakkautawa tare da kona gine-ginen da wata motar sintirin ’yan sanda.

Sojojin da ’yan sandan Rundunar Operation Whirl Stroke da ke Jihar sun kai wa mazauna yankin dauki inda suka yi dauki ba dadi suka kashe daya daga cikin ’yan bindgar suka kuma samu harsasai sama da 200.

Wani mazaunin yankin ya shaida wa Aminiya cewa jami’an tsaro sun yi saurin kawo musu dauki da kuma fatattakar ’yan bindigar duk da cewa a asubahi suka kai harin.

Ana zargin ’yan bindigar da suka kai harin yaran shugaban masu garkuwa da mutane a jihar, margiyar Terwase Akwaza wanda aka fi sani da ‘Gana’ ne.