✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kashe dan sanda da dan banga a Sakkwato

’Yan bindiga sun kashe dan sanda daya da wani dan banga ranar Litinin a Jihar Sakkwato .

’Yan bindiga sun kashe dan sanda daya da wani dan banga ranar Litinin a Jihar Sakkwato .

Da misalin karfe 3 na asuba kafin wayewar gari ne yan bindigar suka kai wa jami’an tsaron da ke sintiri hari a yankin Kwanan Milgoma da ke kan titin Sakkwato zuwa Bodinga.

Wani babban jami’in ’yan sandan da ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar wa wakilinmu cewa, “’Yan bindigar sun hadu da ’yan sandan ne a wani shingen bincike da ke kan hanyar Sakkwato zuwa Bodinga, inda suka bude musu wuta.

“Sun kashe dan sanda daya da wani dan banga sannan suka tafi da bindigogi kirar AK-47 guda biyu.

“An kai gawarwakin dakin ajiyar gawa na Asibitin Koyarwa na Jami’ar Usmanu Danfodiyo,” in ji shi.

A cewarsa, ’yan bindigar sun kama jami’an ne a cikin wata farar kirar Hilux.

Ba mu samu Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Sakkwato ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.