✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kashe dakarun soji 7 a Katsina

’Yan bindigar sun yi wa sojojin kwantan-bauna, suka bude musu wuta.

Akalla dakarun soji bakwai ne suka rasa rayukansu a wani harin da ’yan bindiga suka kai a Jihar Katsina.

An rawaito cewa an kashe dakarun sojin ne a kauyen Kadobe da ke da tazarar kilomita hudu da kauyen Kukar Babangida a Karamar Hukumar Jibiya a jihar Katsina.

Dakarun sojin sun bi bayan ’yan bindiga ne bayan sun yi fashin wasu dabobbi a wasu kauyuka na Najeriya kuma suka yi yunkurin tsallake iyakar Najeriya da su.

Wani mazaunin yankin ya ce har yanzu ba a san adadin sojojin da suka mutu a dalilin harin ba.

“Mun gano cewa da ’yan bindiga da su fasin sun fahimci cewa sojoji na bin su sai suka yi kwanton-bauna suka bude musu wuta suka kashe bakwai daga cikin sojojin.

“Wadanda ba a kashe ba sun nemi karin dakaru, kuma sun bi bayan ’yan bindigar amma har yanzu ba mu da masaniyar abin da ya faru,” a cewarsa.

Aminiya ta rawaito yadda mazauna yankunan da ke iyakar Najeriya da wasu kasashe ke fuskantar hare-hare ’yan bindiga, sannan koyaushe suna neman dauki daga jami’an tsaron Najeriya.