’Yan bindiga sun kashe wani basarake, Eze Ignitus Asor, tare da wasu mutum hudu a kauyen Obudi Agwa da ke Karamar Hukumar Oguta a Jihar Imo.
Harin, wanda ya auku a ranar Litinin, na zuwa ne kwanaki kadan bayan an sami arangama tsakanin sojoji da matasan Izombe da ke yankin.
- NAJERIYA A YAU: Saukar Farashin Hatsi Ba Za Ta Dore Ba —Masani
- Yadda Soludo ya yi wa Peter Obi wankin babban bargo
Aminiya ta kalato cewa, wasu matasan yankin dauke da bindigogi sun dira fadar sarkin da aka alakanta da rikicin da ya faru tsakanin mazauna yankin, sannan suka bude wuta.
An ce nan take sarkin da fadawansa biyu suka ce ga garinku nan, yayin da wasu suka ji rauni sakamakon harbin bindiga.
Kazalika, majiyarmu ta ce matasan sun shiga kauyen Mgbala inda a nan aka ce sun kashe wata mata mai juna-biyu da wani jami’in tsaron yankin.
Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ’Yan Sandan Jihar, CSP Mike Abattam, ya tabbatar da aukuwar lamarin.
Abattam ya ce binciken farko ya gano matasan sun zo ne a cikin motoci hudu da babura biyu, kuma har da mace a cikinsu.
Ya kara da cewa, babu wata tirjiya sarkin ya bar matasan suka shiga fadarsa suka zauna domin jin dalilin da ke tafe da su.
Ya ce a daidai wannan lokaci ne matasan suka fito da bindigogi suka bude masa tare da fadawansa wuta.