’Yan bindiga sun kashe wani ango tare da yi awon gaba da amaryarsa a garin Jere da ke Karamar Hukumar Kagarko ta Jihar Kaduna.
Ganau sun ce ’yan bindiga kusan 50 a kan babura ne suka yi wa garin dirar mikiya, suka shafe kusan awa uku suna cin karensu babu babbaka, suka dauke matar tsohon Kwamishinan Yaki da Talauci na Jihar Kaduna, Abdulrahman Ibrahim Jere.
- Kudaden da daliget ke karba zai iya kai su wuta —Dan takara
- APC ta dage taronta na zaben dan takarar shugaban kasa
Rahotanni daga garin Jere sun ce a daren ranar Juma’a ne ’yan bindigar suka rika bi gida-gida, amma bisa alama gidan tsohon kwamishinan ne hadafinsu.
Sun bayyana cewa baya ga amaryar da aka kashe angonta aka tafi da iya, maharan sun yi awon gaba da matar tsohon kwamishinan da ’yar da take shaywarsa da a kanwarsa da kuma ’yar uwar matarsa.
Wani mazaunin garin ya bayyana cewa bayan maharan sun shiga gidan sabbin ma’auratan suna kokarin tafiya da amaryar, sai angon ya ki bari su tafi da ita, nan take suka harbe shi har lahira.
Mazauna garin Jere da ke kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna sun bayyana bacin ransu, cewa duk da sojoji da ’yan sanda da sauran jami’an tsaron da ke sintiri a yankin, amma sun kasa daukar mataki a kan ’yan bindigar da suka shafe kusan awa uku suka cin karensu babu babbaka a garin.
“Mun kira duk jami’an tsaron da ke yankin sau shurin masaki, amma suka yi watsi da kiran da muka yi musu.
“Wannnan shi ne babban hari na biyu da aka kawo mana a cikin wata uku kuma muna ganin jami’an tsaron da aka girke a nan ba su da wani amfani,” inji wani mazaunin garin.
Shi ma wani mazaunin garin, ya ce za su rubuta korafi a hukumance kan jami’an tsaron da ke yankin, saboda take-takensu na nuna, “Ko suna hada banki da ’yan bindiga ko kuma ba su damu da tsaron jama’a ba.”
A cewarsa, sai da aka shafe awoyi bayan tafiyar ’yan bindigar da suka kai harin kafin jami’an tsaro suka bi sawun maharan, daga baya suka sanar da su cewa sun kashe biyu daga cikin bata-garin.