’Yan bindiga sun sake kashe mutum tara awanni kadan bayan sun kashe mutum 6 ciki har da yaro mai shekara 7 a Karamar Hukumar Giwa, Jihar Kaduna.
Mazauna sun shaida wa Aminiya cewar a daren Lahadi ne maharan suka shiga kauyen suna harbe-harbe tare da kona gidaje da motoci da babura.
- Dan majalisa ya tsallake rijiya da baya a Kudancin Kaduna
- Sojoji sun kashe ’yan bindiga sun kwato mutum 23
“Bayan sun kai hari a kauyen Kidandan a daren Juma’a, sojojin kasa da na sama da kuma ’yan sanda sun kai samame ta sama, sauran kuma suka shiga da tankokin yaki ta kasa.
“Mun ji an ce jami’an tsaron sun kori ’yan bindiga, har sun kashe wasunsu, amma sai suka kara taruwa suka kai sabon farmakin a kauyen Kadai”, inji wani shigaban matasa, Hussaini Umar.
Umar ya ce maharani sun tare hanyar Gwargwaji-Dogon Dawa a lokacin da suke aika-aikar.
Ya ce mutanen kauyen da dama sun bace wasu daruruwa kuma sun yi kaura zuwa garin Galadimawa da Zariya da ke kusa da su.
Kilomita uku ne tsakanin kauyen Kidandan inda aka fara kai harin da kuma Kadai inda daga baya aka kashe mutum tara – duk a gundumar Fatika da ke karamar hukumar.
Wani bincike ya nuna cewar yawaitar farmakin na da nasaba da kama wani dan bindiga da ’yan banga suka yi a yankin suka damka wa jami’an tsaro.
Wata majiya a Fatika da Galadimawa ta shaida mana cewar daya daga cikin ’yan bindigar da aka mika wa jami’an tsaro an kama shi ne sanye da kayan sojoji da muggan makamai.
Kakakin Rundunar ’Yan Sanda Jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige, bai amsa kiran wakilinmu ta yawa ba, amma gwamnatin jihar ta yi wa mutanen Kadai da Kidandan ta’aziya ta kuma yi kira ga jami’an tsaro da su ci gaba da kokarinsu na dakile ta’addanci a yankin.
A sakon da Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida, Samuel Aruwan ya fitar, ya ce jami’an tsaro sun kashe yan ta’ada da ba a san adadinsu ba a Kidandan, wasunsu kuma sun tsere da raunukan harbin bindiga.
Ana fargabar ’yan bindiga masu alaka da kungiyar ’yan ta’adddan ISWAP sun hallaka mutane da dama a yankin.
In ba a manta ba, ’yan bindiga, a watan Maris, sun kai farmaki a kauyuka biyar da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 51 a yankin.
Shuaban ’Yan Sandan Najeriya, Mohammed Adamu, a ziyarar da ya kai ya alakanta ’yan bindigar da kungiyar ISWAP.