’Yan bindiga sun kai hari kan wani ayarin maniyyata Aikin Hajji da ke fitowa daga Karamar Hukumar Isa ta Jihar Sakkwato ranar Litinin.
Maniyyatan dai na kan hanyarsu ce ta zuwa birnin Sakkwato, don shirin tashi zuwa kasa mai tsarki da misalin karfe 7:30 na safiyar Talata.
- ‘Macizai sun fara saran fasinjojin jirgin kasan da ke hannun ’yan bindiga’
- Tukunyar gas din mai shayi ta kona mutum 23 a Lere
Maharan dai sun kai farmakin ne kan ayarin a daidai dajin Gundumi, amma jami’an tsaro suka dakile yunkurin nasu.
Wani mazaunin garin Isa, Malam Sirajo, ya shaida wa Aminiya cewa maniyyatan sun kubuta daga harin ba tare da ko kwarzane ba, yayin da aka dawo da wasu daga cikinsu Fadar Sarkin Gobir Isa.
Ya ce, “Sun kai wa ayarin farmaki ne lokacin da suke cikin rakiyar jami’an tsaro, inda suka yi musayar wuta na wasu ’yan mintuna.
“Mun gano cewa wasu daga cikin jami’an tsaron sun ji raunuka, amma ba zan iya tabbatar da hakan ba, inji Sirajo.
Shi ma Shugaban Hukumar Bayar da Tallafin Karo Karatu ta Jihar ta Sakkwato, Shehu Muhammad Dange, ya tabbatar da faruwar lamarin, amma ya ce ba zai iya sanin ko an saci wasu daga cikinsu ba ko kuma a’a.
Sai dai Kakakin Gwamnan Jihar Aminu Waziri Tambuwal, wato Muhammad Bello ya tabbatar da kai harin, amma ya ce an ceto ilahirin maniyyatan ba tare da ko kwarzane ba.
A cikin wata sanarwa da ya fitar da yammacin Litinin, kakakin ya ce, “Kwamishinan Yada Labarai na Jihar, Isah Bajini Galadanchi, ya ce dukkan maniyyatan da ’yan rakiyarsu sun isa birnin Sakkwato lami lafiya.
“Tuni jami’an gwamnati suka karbe su, kuma suna shirye-shiryen tashi zuwa kasa mai tsarki [gobe] da safe,” inji sanarwar.
Sai dai da wakilinmu ya tuntubi Kakakin ’yan sandan Jihar, ASP Ahmad Rufa’i, ya ce ba su da masaniya a kan harin.