✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun kai harin daukar fansa kan mayakan Boko Haram a Kaduna

’Yan bindiga da dama sun kwanta dama yayin artabu da mayakan Boko Haram.

Rahotanni sun bayyana cewa ’yan bindiga sun kai wani hari na daukar fansa kan mayakan Boko Haram a kauyen Damari da ke Karamar Hukumar Birnin Gwari a Jihar Kaduna.

Daruruwan mutane dai sun tsere yayin da gomman ’yan bindigar haye a kan babura suka kai hari kan al’ummar Damari da ke Karamar Hukumar ta Birnin Gwari.

Mazauna sun shaida wa Aminiya cewa ’yan bindigar da suka kai hari da safiyar ranar Lahadi, sun biyo sahun magoya bayan wani jagoran ’yan ta’adda ne mai suna Malam Abba, wanda tun a shekerar 2020 rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna ta tabbatar da cewa dan Boko Haram ne.

Ibrahim Hassan, wani mazauni a Damari kuma daya daga cikin mutanen da suka tsere, ya ce ’yan bindigar sun shigo garin ne da misalin karfe 10 na safiyar Lahadi, inda nan take mutane suka fara cika bujensu da iska domin neman tsira sakamakon sautin harbe-harben da ya razana su.

Bayanai sun ce an yi wata mummunar arangama ranar Juma’a tsakanin ’yan bindiga da mayakan Malam Abba, inda ’yan bindiga da dama suka kwanta dama.

Wata majiya a yankin ta ce, yunkurin daukar fansa ne ya sanya ’yan bindigar suka kai hari Damari a matsayin ramuwar gayya kasancewar Malam Abba ke bai wa al’ummarsu kariya.

ASP Mohammae Jalige, kakakin ’yan sandan Jihar Kaduna da wakilinmu ya tuntuba, ya ce tuni aka umarci ’yan sanda da ke kula da yankin da su jibinci lamarin.

Har yanzu dai hare-haren ’yan bindiga na ci gaba da tsananta a Jihar Kaduna duk da ayyukan da dakarun soji ke ci gaba da gudanarwa a jihar da wasu sassan a Arewacin kasar don ganin an murkushe ’yan ta’adda.

%d bloggers like this: